Featured
Buhari ya yi min alkawarin ba ni tikitin takarar shugaban ƙasa na APC a 2022 — Amaechi
Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi masa alkawarin ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa na APC a zaɓen 2022, amma daga bisani ya rasa tikitin.
Amaechi ya ce ya rasa damar ne sakamakon bin shawarar da Buhari ya ba shi na kada ya gudanar da kamfen kafin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
Read Also : Da ba mu cire tallafin man fetur ba da yanzu ana jigilar Naira a amalanke – Tinubu
Jaridar Punch ta rawaito cewa Amaechi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon Mainland 98.3FM da ke Legas a ranar Juma’a.
Ya kuma yi tsokaci kan yadda Shugaba Bola Tinubu ya kayar da shi a zaɓen fidda gwani na APC a shekarar ta 2022.

Pingback: Ya kamata gwamnatin Tinubu ta fito ta bayyana adadin ƴan Najeriya da ta fitar daga talauci - Peter Obi - KAKAKI 24