Featured
Da ba mu cire tallafin man fetur ba da yanzu ana jigilar Naira a amalanke – Tinubu
Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa da gwamnatinsa ba ta cire tallafin man fetur ba a lokacin da ta karɓi mulki, da darajar Naira ta fadi kasa warwas, da yanzu ana jigilarta a amalanke.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin liyafar girmamawa da aka shirya masa a birnin Uyo, jihar Akwa Ibom, bayan gangamin jam’iyyar APC a filin wasa na Godswill Akpabio, ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, 2026.
Read Also : NAWOJ Kano condoles former NUJ chairman, comrade Abbas Ibrahim, over Mother’s death
A cewar wani rahoto da Channels Television ta wallafa, shugaban ya kare matakan sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatinsa, yana mai cewa cire tallafin man fetur ya zama wajibi domin hana durƙushewar darajar kuɗin ƙasar.

Pingback: Buhari ya yi min alkawarin ba ni tikitin takarar shugaban ƙasa na APC a 2022 — Amaechi - KAKAKI 24