Featured
Wike ga ’yan APC: Kada ku bari ADC da NDC su samu kashi 25 cikin 100 na ƙuri’u a Abuja
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya buƙaci mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da ƙungiyar Rainbow Coalition da su tabbatar da cewa jam’iyyun adawa, musamman ADC da NDC, ba su samu kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da za a kaɗa a Abuja a zaɓen 16 ga Janairu, 2027 ba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Wike ya yi wannan kira ne yayin da yake jawabi ga mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen da ƙungiyar, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai da ƙara ƙaimi wajen ganin APC ta samu gagarumar nasara a babban zaɓen mai zuwa.
Read Also : Najeriya na asarar maƙuden kuɗaɗe saboda haramta tabar wiwi – Sowore
Ministan ya kuma buƙaci masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC da su ƙara jajircewa wajen ganin sun cimma burin jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
Ya jaddada cewa ya kamata mambobin jam’iyyar su tabbatar da cewa jam’iyyun adawa ba su samu goyon bayan masu zaɓe a Babban Birnin Tarayyar Najeriya ba.

Pingback: Amurka na bai wa sojojin Najeriya bayanan sirri gabanin zaɓen 2027 – Ministan Tsaro - KAKAKI 24