Featured
Zaɓen 2027 zai nuna wa duniya ƙarfin jam’iyyar PDP a Jigawa – Sule Lamido
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya bayyana cewa babban zaɓen shekarar 2027 ne zai tabbatar da ƙarfin siyasar jam’iyyar a jihar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Lamido ya bayyana hakan ne ranar Laraba, yayin bikin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen PDP da miƙa tutocin jam’iyyar ga ’yan takararta a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
Read Also : Senator Kawu Sumaila Commends Kano Drug Task Force, Donates ₦5m to Operatives, Supports Rescued Children
An gudanar da taron ne a mazabar sanatan Jigawa ta Kudu maso Yamma, inda aka miƙa tutar jam’iyyar ga ɗan takararta na gwamna, Mustapha Lamido, da ɗan takarar kujerar sanata da sauran ’yan takara.
Lamido ya ce sakamakon babban zaɓen shekarar 2027 ne zai nuna irin ƙarfin da PDP take da shi a fagen siyasa a Jihar Jigawa.

Pingback: Tinubu ya ƙara yawan adadin jihohin da zai halarta domin gangamin ƴakin neman zaɓensa - KAKAKI 24