Connect with us

Featured

Al’ummar Musulmi Su Dage Da Karanta Alqur’ani Tare Da Aiki Dashi – Sarkin Kano

Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero, yayi kira ga al’ummar musulmi da su dage da karanta Al-qur ‘ani maigirma da kuma aiki da abinda yazo dashi.

Kiran ya fito ne ta bakin Wazirin Kano Alh. Sa’ ad Shehu Gidado, wanda ya wakilci Mai Martaba sarki, a wajan taron bikin cikar Makarantar Najahi Islamiyya Sanin Kwano Aisami bangaren dare Shekara 45 da da kafuwa.

Shugaban Makarantar Gali Murtala Sadis, ya bayyana cewa sun shirya taron ne don nuna farin cikin su da wannan nasara ta cika shekaru 45 da kafuwar makarantar.

Tare da wayar da kan yan baya wajan ganin sun cigaba da wannan aikin alkhairy.

Haka zalika ya bayyana cewa sun samu nasarorin da ba za su lissafu ba, daga ciki akwai bude rassa da wasu daga cikin daliban makaranta suka yi.

Ya ƙara da cewa fatan su anan gaba shine a samar da sakandire a cikinta.

Daga ƙarshe ya yi godiya ga dukkan al’ummar da suka halacci taron da fatan Allah ya maida su gidajensu lafiya.

Wakilin mu ya ruwaito mana cewa taron ya samu halartar manyan baki da kuma manyan malamai wanda suka haɗa da khalifah sheikh Sani Hassan Kafinga da Sayyadi Bashir Sheikh Tijjani Usman Zangon Barebari da Sheikh Malam Abdullahi Uwais Limanci da kuma Alh. Muhammad Adawi Dokajin kazaure.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet