Labarai
Marigayi Sarki Ado Bayero ya cika shekaru 9 da rasuwa
A yau Talata 6 ga watan Yuni ne marigayi Sarkin Kano Alhaji Dakta Ado Bayero ya cika shekaru 9 da rasuwa.
A rana irin ta yau, 6 ga Yunin shekarar 2014 ne Allah ya yi wa sarkin rasuwa wanda ya kasance sarki na 13 a daular Fulani.
Marigayin sarkin, ya rasu ne yana da shekara 84 a duniya.
An dai haifi Marigayi Alhaji Dr. Ado Bayero, ne a ranar 25 ga watan Yulin shekara 1930.
Arewa Radio ta ruwaito cewa, Sarkin ya hau karagar mulki ne daga shekara ta 1963 har zuwa rasuwarsa a shekara ta 2014.
Haka kuma ta wallafa cewa, Margayi Ado Bayero, kafin ya zama sarkin kano shahararren ɗan kasuwa, kuma yayi aikin banki, sannan tsohon ɗan sanda ne kuma ya yi aiki a matsayin jakadan Najeriya a ƙasar Senigal.
