Connect with us

Featured

EFCC ta sake maka Emefiele a kotu kan wasu sabbin tuhume-tuhume

Har yanzu dai Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, na fuskantar sabbin tuhume-tuhume guda hudu daga EFCC.

EFCC ta zargi Emefiele da buga kudi Naira miliyan 684.5 ta hanyar kashe Naira biliyan 18.96.

A sabbin tuhume-tuhumen da ta shigar, ta jaddada cewa tsohon gwamnan na CBN ya saba doka tare da karkatar da dukiyar jama’a a karkashin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Ta kuma zargi Emefiele da cire Naira biliyan 124.8 daga asusun tara kudaden shiga (CRF) na tarayya ba bisa ka’ida ba.

Matuƙar na gaza gurfanar da Yahaya Bello to zan yi murabus daga muƙamina – Shugaban EFCC

A cikin takarda mai kwanan wata 2 ga watan Afrilu, 2024 mai lamba: CR/264/2024, mai gabatar da kara daga tsagin EFCC, Rotimi Oyedepo, ya bayyana cewa za a gurfanar da tsohon gwamnan CBN a gaban mai shari’a Hamza Muazu na babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Ana sa ran Emefiele ya kare kansa kan sabbin tuhume-tuhume guda hudu da suka haɗa da karya doka, cire kudi ba bisa ka’ida ba, almundahana da karkatar da dukiyar al’umma.

Tun a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2023 ne, EFCC ta gurfanar da Emefiele a gaban kotu bisa tuhume-tuhume shida da suka shafi almundahana.

Ta kuma zarge shi da rashin bin ka’idar ofishinsa ta hanyar amincewa da kwangilar sayen motoci 43 da kudinsu ya kai Naira biliyan 1.2 daga shekarar 2018 zuwa 2020.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet