Connect with us

Featured

Wutar Lantarkin Najeriya Ta Sake Lalacewa

Da tsakar ranar yau Talata ne babban layin wutar lantarki na Najeriya ya sake lalacewa wanda ya jefa ɗaukacin sassan kasar cikin halin duhu.

Ko a watan da muka yi bankwana da shi na Oktoba an samu lalacewar babban layin lantarki kusan sau uku inda gwamnatin tarayya ta yi alkawarin magance wannan matsala.

Da misalin karfe 2:35 na rana, babu wani kamfanin rarraba wutar lantarki da ke da wuta a faɗin ƙasar nan.

Karanta: Shugaba Tinubu ya rantsar da sabbin ministocinsa

A ranar Asabar, 19 ga Oktoba bana ne cibiyar samar da wutar lantarki ta kasa ta fuskanci babban koma baya, wanda ya nuna gazawarta bayan katsewar babban layin lantarkin a karo na takwas a cikin shekarar nan da muke ciki ta 2024, inda uku suka faru cikin mako guda.

Sai dai a nata ɓangaren, hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta ƙasa NERC ta yi Allah wadai da yadda matsalar wutar lantarki ke kara tabarbarewa a jihohi da dama inda hakan ke kawo koma baya ga dimbin nasarorin da aka samu a baya-bayan.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet