Featured
Likitocin Asibitin Murtala sun sanar da tsunduma yajin aiki
Kungiyar likitoci ta kasa NMA, ta sanar da dakatar da duk wasu aikin kula da marasa lafiya a asibitin kwararru na Murtala Muhammed biyo bayan shafe sa’o’i 24 ba tare da gwamnati ta dauki mataki a kan kwamishinar harkokin jin kai ta Kano Hajiya Amina HOD, sakamakon zarginta da cin zarafin wata likita.
Kungiyar NMA ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Kano Dakta Muhammad Aminu Musa, ya fitar da yammacin yau Laraba.
Sanarwar ta kungiyar NMA, ta gindaya wasu sharuda uku ga gwamnatin Kano a matsayin hanyar janye wa daga tsunduma yajin aikin na sai Baba ta gani.
Sharudan sun hada da:
Korar kwamishinar kwamishinar harkokin jin kai daga kan mukaminta.
Samar wa jami’ain lafiya yanayin aiki mai kyau ta yadda za su rika yin aikin ba tare da takura ko kuma musgunawa ba.
Samar da ingantaccen tsaro domin kula da jami’an lafiya da kuma marasa lafiya a dukkan sassan asibitin kwararru na Murtala Muhammad.
Haka kuma ta cikin sanarwar, kungiyar likitocin ta kasa NMA shiyyar Kano, ta ta jaddada kudurinta na tabbatar da yin aiki cikin kwarewa tare da bayar da kulawa ta musamman amma dai, wannan matsala da ta kunno kai ta tilasta mata dakatar da aiki har zuwa lokacin da gwamnatin Kano za ta dauki matakin da ya dace.
