Featured
EFCC ta kori jami’an ta 27 bisa zargin aikata zamba
Hukumar da Ke Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa, (EFCC), ta kori akalla ma’aikatanta 27 bisa zarginsu da aikata zamba da wasu munanan ayyuka da suka saba wa tsarin aikin hukumar.
Duk da cewa ba a bayyana sunayen jami’an da aka kora ba, an kore su ne bisa shawarar kwamitin da’ar ma’aikata na hukumar ta EFCC, bayan amincewar shugaban hukumar Ola Olukoyede kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito.
Da yake magana game da lamarin, shugaban na EFCC ya ce, hukumar ta himmatu wajen kawar da cin hanci da rashawa, inda kuma yayi gargadin cewa, babu wani jami’in da ya tsira daga matakin na ladabtarwar.
Olukoyede, wanda ya yi magana ta bakin mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, ya ce jiga-jigan manufofin hukumar masu kyau ne, kuma za a rika gudanar da su cikin kyakykyawar fahimta a kowane lokaci.
“Duk wata badakala da aka tuhumi wani ma’aikacin hukumar dole za a rika bincike, ciki har da batun dala 400,000 da har yanzu ake bincike a kai. duka wannan yana cikin shirin mu da kokarinmu na tabbatar da gaskiya da kuma kawar da abubuwan da ke addabar mu” a cewar sa.
