Featured
Najeriya Ta ƙaryata Amurka Kan Zargin Cin Zarafin Kiristoci
Najeriya ta yi watsi da zargin da Amurka ta yiwa ƙasar cewar tana musgunawa mabiya addinin Kirista, saboda haka ya dace a sanya ta cikin jerin ƙasashen dake da matsalar bai wa jama’a ƴancin addini.
Ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Tuggar ya bayyana haka sakamakon zargin da wani ɗan majalisar Amurka Chris Smith ya yi, inda yace ana hana mabiya addinin Kirista ƴancin gudanar da addinin su yadda ya kamata.
Buhari Ya Bayyana Matsayarsa Kan Ci Gaba Da Zama A Jam’iyyar APC
Tuggar ya ce matsalolin tsaron da ake fuskanta a Najeriya ba su da nasaba da addini, ganin yadda suke ritsawa da Musulmi da kuma Kirista.
Ministan ya ce waɗannan hare hare da ake samu a ƴankunan arewa maso gabas da kuma arewa maso yamma basa barin mabiyan wani addini na daban.
Wannan ya sa gwamnatin bayyana damuwa akan yadda ake yaɗa labaran ƙarya dangane da yadda al’amura suke a zahiri akan kashe kashen da ake samu a ƙasar.
Abubuwa Biyar Da Ya Kamata A Yiwa Iyaye Bayan Sun Rasu
Ɗan majalisar Amurka Smith ya bayyana matsayin sa ne sakamakon rahotan wata ƙungiyar agaji ta Kiristoci da ake kira Open Doors wadda ta ce daga cikin kashi 100 na Kiristocin da ake kashewa a duniya, kashi 89 na faruwa ne a Najeriya.
Ita dai wannan ƙungiyar agaji dake aiki a ƙasashen duniya sama da 70, na raba wa mutane littafin Bible ne da kuma kare haƙƙoƙin Kiristocin da ake cin zarafin su.
A na shi tsokacin, Daraktan Ƙungiyar Amnesty a Najeriya, Isa Sanusi ya ce ba daidai bane wannan labari dake cewa Kiristoci aka fi kashewa a rikice rikicen da ake samu a Najeriya.
Sanusi ya ce an ma fi kashe Musulmi akan Kiristoci, yayin da ya kara da cewa babu wani addini da maharan basa kashewa duk lokacin da suka kai hari, saboda haka wannan matsayi na iya jefa ruɗani da kuma tankiya a tsakanin jama’ar ƙasar.
Ko a lokacin mulkin Trump na baya, sanda aka sanya sunan Najeriya cikin ƙasashen dake hana Kiristoci gudanar da addinsu.
