Connect with us

Featured

Buhari Ya Bayyana Matsayarsa Kan Ci Gaba Da Zama A Jam’iyyar APC

Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce har yanzu shi ɗan Jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar ne, kuma ya fi so a rinƙa alaƙanta shi da ita.

A Wata sanarwa da tsohon kakakinsa, Garba Shehu ya fitar ranar Alhamis ta ce “ba tare da ba da misali da kowane mutum ko wasu matsaloli ko aƙidoji da shugabannin jam’iyya ke tattaunawa a kansu ba a matakai daban-daban, Muhammadu Buhari ya jaddada batun da ya sha faɗa cewa shi ɗan APC ne, kuma yana so a dinga alaƙanta shi da zama mamban jam’iyyar na gani-kashe-ni.

Hakan na zuwa ne bayan wata hira da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi da BBC Hausa ranar Alhamis, kwanaki kaɗan bayan ficewarsa daga APC, inda ya ce da amincewar Buhari ya bar jam’iyyar ta APC zuwa SDP.

Sanarwar ta ƙara da cewa tsohon shugaban ƙasar ya ce ba zai taɓa juya wa jam’iyyar da ta ba shi damar tsayawa takara baya ba har ya yi shugabancin ƙasa na wa’adi biyu.

“Ni ɗan APC ne, kuma na fi so ana alaƙanta ni da jam’iyyar, sannan zan yi duk mai yiwuwa wajen tallata jam’iyyar.”

Muhammadu Buhari ya kuma ƙara da cewa a yanzu haka babu abin da zai ce game da jam’iyyar APC sai dai godiya bisa goyon bayan da ya samu daga gare ta, a lokacin da yake mulki da bayan ya kammala wa’adinsa, wanda a cewarsa alfarma ce babba da ba zai taɓa mantawa ba.

Sannan ya ce wahalar da waɗanda suka kafa APC suka sha yayin samar da jam’iyya mai ƙarfi domin kare martabar kundin tsarin mulki da dimokuraɗiyya ba za ta tafi a banza ba.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantmatbetholiganbetholiganbet girişcasibomvdcasinosahabetmarsbahismarsbahis girişholiganbetholiganbet girişcasibomcasinolevantcasinolevantcasibomsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet