Featured
Dokar Ta-ɓaci: Fubara Ya Fice Daga Gidan Gwamnatin Jihar Rivers
Gwamnan Jihar Rivers da aka dakatar, Similanayi Fubara, ya fice Fadar Gwamnatin Jihar da ke Fatakwal.
Majiyar mu ta tabbatar da cewa Fubara ya fice daga Fadar Gwamnatin da safiyar Laraba, a daidai lokacin da sabon Shugaban Riƙn Ƙwarya, Admiral Ekwe Ibas (mai ritaya), ke shirin karɓar ragamar mulki.
Majiyar tamu ta tabbatar da cewa akwai kwanciyar hankali a yankin, inda aka girke motocin yaƙi guda uku a kofar shiga gidan gwamnatin.

Gidan gwamna yin jihar Rivers
Wani jami’in tsaro ya tabbatar da cewa an sauya dukkanin jami’an tsaron da ke aiki a Fadar Gwamnatin Jihar.
Majalisar Dattawa Ta Dage Amincewa Da Kudirin Dokar Ta-ɓaci A Jihar Rivers
“Gwamna ya fice daga ciki, kuma muna jiran sabon shugaba ya iso. Komai na tafiya lafiya,” in ji shi.
A halin yanzu, al’ummar Fatakwal na ci gaba da harkokinsu yadda suka saba ba tare da wata matsala ba.
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas a ranar Talata, sakamakon rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar.
Sai dai matakin na Shugaban Ƙasa, ya bar baya da ƙura inda mutane ke tofa albarkacin bakinsu kan lamarin.
