Connect with us

Featured

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Dokar Ta-ɓacin Da Tinubu Yasa A Rivers

Majalisar Wakilai ta amince da ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaban Kasa Bola Tinubu yasa a Jihar Rivers.

Majalisar ta yanke wannan shawara ne a ranar Alhamis din nan, ta hanyar kaɗa ƙuri’a da baki, inda ’yan majalisa 243 suka halarta.

A matsayin wani ɓangare na matakan dokar ta-ɓaci, majalisar ta bayar da shawarar kafa kwamiti domin dawo da zaman lafiya a jihar.

Hakazalika, majalisar za ta karɓi ragamar gudanar da ayyukan Majalisar Dokokin Jihar Ribas na tsawon watanni shida.

Me Ya Janyo Ayyana Dokar Ta-ɓacin?

Matakin ya biyo bayan rikicin siyasa da ya ƙi ya ƙi cinyewa a Jihar Ribas.

Shugaba Tinubu ya yanke wannan shawara ne sakamakon tashe-tashen hankula da rikicin shugabanci a jihar.

Gwamna Siminalayi Fubara na takun-saƙa da Majalisar Dokokin Jihar da wasu jiga-jigan ’yan siyasa musamman waɗanda ke tsagin tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, lamarin da ya jefa jihar cikin tashin hankali.

Domin shawo kan matsalar, Tinubu ya naɗa Tsohon Babban Hafsan Rundunar Sojin Ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin sabon mai kula da jihar.

Hakan ya sa Gwamna Fubara da wasu manyan jami’ai, ciki har da iyalansa, suka bar gidan gwamnatin jihar.

Ana ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki a jihar, yayin da gwamnati ke ƙoƙarin tabbatar da doka da oda a jihar.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet