Featured
Shugaban Ghana Ya Ziyarci Tawagar Ƙwallon Kasar Don Ƙarfafa Musu Gwiwa
Shugaban Kasar Ghana John Dramani Mahama ya kai ziyara ga tawagar kungiyar ƙwallon ƙafa ta Ghana, Black Stars gabanin wasansu da tawagar Chadi don neman buga gasar cikin Kofin Duniya ta 2026.
A ƙoƙarin ƙara karsashin tawagar ƙwallon ƙafa ta Ghana, Black Stars gabanin wasannin neman buga Gasar Kofin Duniya ta FIFA, Shugaba John Dramani Mahama ya kai wa tawagar ziyarar ƙarfafa gwiwa a ranar Laraba, 19 ga Maris.
Black Stars na shirin karawa da tawagar ƙasar Chadi, da kuma ta Madagascar domin neman cancantar buga Gasar Kofin Duniya da za a yi a 2026.
Hukumar Kwallon kafa ta Ghana ta wallafa a shafinta cewa shugaban Ghana ya kai ziyarar a filin wasa na Accra Sports Stadium, da niyyar ƙara azama ga tawagar da ke fuskantar wasanni masu muhimmanci.
Shugaba Mahama ya nemi ‘yan wasan da su ɗaga martabar Ghana ta hanyar nuna bajintarsu da ƙwarewarsu a fagen ƙwallon ƙafar ƙasa-da-ƙasa.
Dabi’ar nasara
Mahama ya tunatar da su muhimmancin ladabi, da aiki tuƙuru da haɗin-kai, inda ya ce waɗannan ɗabi’u suna da tasiri wajen cim ma nasara a ƙwallon ƙafa.
‘Yan wasan tawagar ta Black Stars, da masu horar da su, da sauran jami’ai sun yi maraba da ziyarar shugaban, kuma sun bayyana godiyarsu kan goyon bayan da ya ba su.
A ranar Juma’a 21 ga Maris ne Black Stars za ta fuskanci Chadi a filin wasa na Accra Sports Stadium. Daga bisani ranar Litinin 24 ga Maris, za ta tafi Morocco don karawa da tawagar ƙasar.
