Featured
Boko Haram: An Hallaks Jami’in Ɗan Sanda A Wani Sabon Harin Jihar Borno
Wani Jami’in ɗan sanda mai mukamin Sufeta ya Rasa ransa a yayin wani kwanton ɓauna da wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne suka kai a kwalejin horar da rundunar ’yan sanda (PMFTC) Camp Limankara, ta Gwoza a Borno.
Majiyoyin leƙen asiri sun shaidawa majiyar Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 0600 a ranar 3 ga watan Afrilu, 2025, yayin da tawagar jami’an tsaro da suka haɗa da na makarantar horas da ’yan sanda ta Mopol Gwoza da wasu sassan rundunar ’yan sanda ke sintiri a ƙafa.
Sufeta Andrawus Musa da ke aiki a runduna ta 6PMF a Maiduguri ya samu munanan raunuka yayin harin yayin da maharan suka ƙwace bindigarsa ƙirar AK-47.
Nan take aka wuce da Andrawus zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) amma daga bisani an tabbatar da rasuwarsa.
Tuni dai aka ajiye gawar a asibiti domin a tantance ta wadda daga bisani za a yi mata jana’iza.
