Featured
Kuyi Hattara Da Ƴan Damfara, Har Yanzu Ba’a Fara Daukar Sabbin Ma’aikata A “Fire Services” Da “Immigration” Ba – Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta nesanta kanta daga wata takardar daukar aiki da ake yadawa a kafafen sada zumunta, inda ta gargadi ‘yan Najeriya, musamman masu neman aikin yi, da su yi taka-tsantsan kada su fada cikin tarkon masu damfara.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a yau Talata 11 ga Yuni, Hukumar Kula da Tsaro ta cikin Gida, Gyaran Halin Kurkuku, Harkokin Wuta da Shige da Fice, Sakataren Hukumomin AM Jibril, ya bayyana cewa, duk da cewa Shugaban kasa ya amince da daukar ma’aikata a cikin wadannan hukumomi hudu na paramilitary, har yanzu ba a fara daukar ma’aikatan ba.
Hukumar ta kara jaddada cewa duk wata sanarwa ta gaskiya game da daukar ma’aikata zata fito ne ta jaridun kasa da sauran kafafen yada labarai na gaskiya, sannan ba za a karbi kudade daga kowane mataki na daukar ma’aikata ba.
Sanarwar ta ce: “Hankalin Hukumar Civil Defence, Correctional, Fire Services da Immigration ya kai kan wata wasika da ke yawo a kafafen sada zumunta game da daukar ma’aikata.
“Yana da muhimmanci a sanar da jama’a cewa, duk da amincewar Shugaban kasa wajen daukar ma’aikata a hukumomin paramilitary hudu da suke karkashin kulawarta, akwai wasu matakai masu yawa da ake bi kafin fara daukar ma’aikatan.
“Hukumar tana son ta kara jaddada cewa dukkan matakan daukar ma’aikata za su fito ne a jaridun kasa, sannan za a gudanar da shi cikin gaskiya da adalci ba tare da karbar kudi daga kowa ba.
“An shawarci jama’a da su yi watsi da wannan wasikar bogi tare da kasancewa masu lura da ayyukan masu damfara da ke kokarin yaudara ‘yan kasa marasa masaniya.
“Don haka, ana rokon jama’a da su yi taka-tsantsan kada su fada tarkon masu damfara da ke son karbar dukiyarsu ta hanyar yaudara.”
