Featured
Gwamnatin Kano Ta Shirya Taron Bita Ga Jami’an Yaɗa Labarai Kan Amfanin Abinci Mai Gina Jiki
)Gwamnatin Kano ta shirya taron bita na yini biyu ga jami’an yada labari da ke kananan hukumomin jihar.
Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Jihar Kano ce ta shirya taron da hadin gwiwar Kungiyar da ke kula da yadda ake samar da abinci mai gina jiki reshen jihar Kano da kuma Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano.
Taron wanda aka gudanar a ranar Litinin 30 ga Yuni 2025, a dakin taro na Babale Suit da ke Nassarawa GRA a Kano, an shirya shi ne domin wayar da kan jami’an yada labarai ta yadda za su isar da sako game da amfanin abinci mai gina jiki a kananan hukumomin su.
Taron ya samu halartar Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya da masana harkar kiwaon lafiya da kuma jami’an yada labarai.
Da yake jawabai yayin taron, Comr. Waiya ya ce sun shigo da jami’an yaɗa labarai cikin harkar lafiya ne saboda su ne su ke saurin isar da sakonni ga alummomin yankin su ta yadda za a magance matsalolin rashin lafiya a kananan hukumomin jihar.
A karshe Waiya ya ce Gwamnatin Kano za ta sanya gasa a tsakanin jami’an yada labarai domin fitar da jami’in da ya fi kwazo a harkar wayar da kan alumma a fadin jihar Kano.
