Featured
ADC Za Ta Fifita Buƙatun ‘Yan Najeriya Akan Komai – Peter Obi
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa gamayyar jamiyyun adawa a Najeriya da su ka rungumi jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) za ta mayar da hankali wajen sanya bukatun yan Najeriya sama da komai wajen gudanar da mulki.
Obi ya sake jaddada goyon bayansa da haɗuwa a jam’iyyar ADC a matsayin dandalin haɗin gwiwa na siyasa gabanin babban zaɓen 2027 da nufin kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga mulki.
A cewar Obi, wannan mataki ya samo asali ne daga ƙudurinsu na kawo shugabanci mai nagarta da tausayi ga Najeriya.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya bayyana haka ne a yau Alhamis 03 ga Yuli 2025, a shafinsa na X, ya bayyana cewa sai da aka yi dogon tunani da nazari kafin aka zabi ADC a matsayin wadda za ta share hawayen yan Najeriya
