Featured
A Yanzu Zan Iya Biyan Shugaban School of Nursing Albashin 500,000 a wata – Rahma Sa’idu

A cikin wani salo na gugar zana, an gano shahararriyar yar TikTok din na, wato Rahma Said, tana cewa za ta iya daukar Shugaban Kwalejin School of Nursing aiki kuma har ta biya shi, duk da tasan Albashin sa bazai wuce 200, 000 zuwa 300,000 a wata ba, inda tace za ta iya bashi 500,000 ma.
Wasu dai na ganin zancen nata baya rasa nasaba da korar matashiyar yar TikTok din da akayi, a Kebbi State College of Nursing Sciences, sakamakon amfani da TikTok ba bisa ka’ida ba, duk da cewa makarantar ta ce ba dalilin manhajar TikTok ta kori matashiyar ba sai saboda wasu dalilai.
Tun bayan korar Rahma dai an hange ta tana bude shagunan sayar da Takalma da Jakunkuna da Riguna a wasu jihohin Najeriya, ciki har da jihar Kano, inda shagon nata ya jawo cece kuce a baya bayan nan.
A yanzu dai ana ganin huce takaici ne Rahman ta yi ga shugaban makarantar, a sabon Videon nata da abokin ta Baba Sadik ya wallafa a shafin sa na Facebook.