Featured
Gwamnatin Zamfara Za Ta Siya Wa Mutane 36,176 Hannayen Jari a Kamfanin Dangote

Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da shirin sayen hannayen jari ga mutum 36,176 daga cikin al’ummar jihar a Kamfanin Dangote, domin ƙarfafa shigarsu harkokin zuba jari na zamani da bunƙasa tattalin arzikinsu.
A cewar Ma’aikatar Harkokin Agaji ta jihar, shirin zai bai wa al’umma damar shiga harkokin zuba jari tare da cin gajiyar damammakin kasuwanci a ƙasar, kamar yadda jaridar Channels ta ruwaito.
Read Also : Ba mu hana ɗalibai mata masu niƙabi shiga makaranta ba – Kwalejin Shari’a ta Aminu Kano
Ma’aikatar ta bayyana cewa ana sa ran kowane wanda zai amfana da shirin zai samu kusan hannayen jari 20, yayin da Kwamishinan Harkokin Agaji na jihar, Salisu Musa Tsafe Kainuwa, zai jagoranci aiwatar da shirin.
Za a zaɓi waɗanda za su amfana daga ƙananan hukumomi 14 na jihar, inda kowace daga cikin ƙananan hukumomi 13 za ta samu mutum 2,261, yayin da Gusau za ta samu mutum 4,522. Gwamnatin ta kuma ce shirin zai haɗa da masu buƙata ta musamman domin tabbatar da ba a bar kowa a baya ba.
Pingback: Gov Buni Inaugurates 2 Commissioners, LG Chairmen; Charges Officials On Service Delivery, Party Loyalty - KAKAKI 24