Featured
Kada ƴan Najeriya su tayar da hankalinsu saboda ɓullar cutar Ebola – Ministan Lafiya

Ministan Lafiya, Dokta Muhammed Ali Pate, ya buƙaci ’yan Najeriya da kada su ɗaga hankalinsu kan cutar Ebola da ta ɓulla a Abuja, yace Gwamnatin Tarayya ta shirya tsaf domin dakile yaɗuwar cutar.
Pate ya bayyana haka ne a fadar shugaban ƙasa ranar Laraba, bayan ganawarsa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila. Inda ya ce an gano mutum ɗaya da ya kamu da cutar.
Read Also : Bauchi: An tsige wani limami saboda zargin tallan Tinubu a Masallaci
Ministan ya ce gwamnati na bin diddigin mutanen da suka yi mu’amala da mai cutar, tare da haɗin gwiwar Uganda da sauran hukumomin lafiya domin shawo kan lamarin.
Ya kuma buƙaci jama’a su bi shawarwarin lafiya daga sahihan majiyoyi, su guji yaɗa labaran ƙarya, tare da tabbatar da cewa NCDC na aiki dare da rana. Ya kuma ce za a sanar da ’yan Najeriya halin da ake ciki idan yanayin ya sauya.
Pingback: FRSC Ta Hana Jami’anta Raka Ƴan Siyasa Yayin Gangamin Yaƙin Neman Zaɓen 2027 - KAKAKI 24