Featured
Ba da yawun mu malaman jami’o’i a Arewacin Najeriya suka goyi bayan Tinubu ba – ASUU

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta musanta batun goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, a cewarta ƙungiyar ba ta siyasa ba ce.
Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya ce malaman jami’a na da ’yancin shiga kowace irin jam’iyyar siyasa, amma hakan ya kamata ya kasance a matsayin ɗaiɗai kun su, ba da sunan ƙungiyar ASUU ba.
Read Also : Zargin Alaƙa Da ’Yan Bindiga: Sanata Shehu Buba ya miƙa kansa ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike
Ya ce ASUU ba ta taɓa amincewa ko goyon bayan ɗan takarar wata jam’iyyar siyasa ba, tare da gargadin mambobinta da kada su jawo sunan ƙungiyar cikin harkokin siyasa. Ya ƙara da cewa, “mu ba ’yan siyasa ba ne, kuma za mu ci gaba da tsayawa a matsayin mu.”
Martanin shugaban ASUU ya biyo bayan wani taro da kimanin malaman jami’a da manyan makarantu 600 daga Arewa suka gudanar, inda suka bayyana goyon bayansu ga tazarcen Shugaba Tinubu a zaɓen 2027. Mahalarta taron sun yaba da wasu tsare-tsaren gwamnatin Tinubu, musamman cire tallafin man fetur da sauye-sauyen kasuwar canjin kuɗi.