Featured
Tinubu ya ƙara yawan adadin jihohin da zai halarta domin gangamin ƴakin neman zaɓensa

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙara yawan adadi jihohin da zai ziyarta domin yaƙin neman zaɓensa na 2027 daga 12 zuwa 19, da birnin tarayya Abuja. Hakan na nufin zai halarci tarukan kamfen din neman tazarcensa guda 20 cikin 37 da jam’iyyar APC ta shirya a faɗin ƙasar.
Sabbin jihohin da aka ƙara cikin jadawalin sun haɗa da Katsina, Taraba, Zamfara, Imo da Kwara, yayin da aka kuma saka Akwa Ibom, Jigawa da Kebbi bayan tarukan kamfen da ya halarta a jihohin a baya-bayan nan.
Read Also : Zaɓen 2027 zai nuna wa duniya ƙarfin jam’iyyar PDP a Jigawa – Sule Lamido
Rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana cewa sauya jadawalin ya biyo bayan buƙatar wasu gwamnonin APC na ganin shugaban ƙasar ya ƙaddamar da ayyukan raya ƙasa a jihohinsu, tare da ƙara yawan fitowarsa wajen kamfen.
Haka kuma, rahoton ya ce matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake tafka muhawara kan shirin Tinubu na halartar kamfen a wasu jihohi kawai, yayin da ‘yan adawa ke sukar matakin na barin shugabannin APC su wakilce shi a sauran jihohin.