Featured
Amurka na bai wa sojojin Najeriya bayanan sirri gabanin zaɓen 2027 – Ministan Tsaro

Ministan Tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya bayyana cewa Amurka na bai wa sojojin ƙasar bayanan sirri na kai-tsaye da hotunan tauraron ɗan Adam domin gano tare da kai hare-hare kan shugabannin ’yan ta’adda gabanin zaɓen 2027.
Musa ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai ranar Litinin, inda ya ce haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu ya taimaka wajen inganta ayyukan sojoji, musamman a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas. Ya ce an kashe shugabannin ’yan bindiga da dama a hare-haren dare.
Read Also : Wike ga ’yan APC: Kada ku bari ADC da NDC su samu kashi 25 cikin 100 na ƙuri’u a Abuja
Ministan ya ce Najeriya na sa ran samun ƙarin jiragen yaƙi masu saukar ungulu daga Amurka da Italiya, yayin da hukumomin tsaro ke ƙarfafa shirin kare zaɓen 2027 kafin gudanar da shi, lokacin zaɓen da kuma bayan kammalawarsa. Ya kuma bayyana damuwa kan amfani da Starlink, kuɗaɗen intanet da jirage marasa matuƙa wajen ayyukan ta’addanci.
Ya ƙara da cewa Najeriya ta cimma yarjejeniya da Kamaru, Nijar da Chadi, wadda ta bai wa sojojin ƙasashen damar bin ’yan ta’adda har zuwa kilomita biyar cikin iyakokin juna. Musa ya kuma yi gargaɗin cewa ƙungiyar IS-Sahel na ƙoƙarin ɗaukar ’yan bindiga a Arewa maso Yamma domin mayar da su masu tsattsauran ra’ayi.