Featured
Majalisar Dokokin Kano Ta Mayar da Martani, Bayan Muhuyi Magaji Ya Zargeta da Jan Ƙafa Kan Ƙudirin Dokar Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi

Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta musanta zargin jan ƙafa wajen nazari da tattauna ƙudirin dokar yaƙi da miyagun ƙwayoyi da Gwamnatin jihar ta gabatar mata, bayan Shugaban Kwamitin Kar-ta-kwana kan Yaƙi da Safarar Miyagun Ƙwayoyi, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, ya nuna damuwa kan jinkirin fara nazarin ƙudirin.
Tun da farko, Muhyi Magaji ya bayyana cewa, sama da makonni biyu kenan tun bayan aika ƙudirin dokar ga majalisar, amma har yanzu ba a fara zaman karatunsa ba. A wata hira da ya yi na tsawon awa ɗaya da rabi a shirin Makwantar Rikici, na gidan Rediyon Lumana, ya nuna damuwa kan abin da ya kira yunƙurin wasu masu ruwa da tsaki na kawo cikas ga dokar saboda saɓanin da ke tsakaninsa da su.
Read Also : Tinubu ya ƙara yawan adadin jihohin da zai halarta domin gangamin ƴakin neman zaɓensa
Lauyan ya jaddada cewa dokar na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da ta’addanci da kuma yaɗuwar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a jihar. Ya kuma yi gargaɗin cewa ba za su bari son ran wasu ya kawo cikas ga ayyukan kwamitin ba, tare da alwashin tunkarar duk mai ƙoƙarin kawo tarnaki ga yaƙin da suke yi da miyagun ƙwayoyi.
Sai dai a martaninta, majalisar ta bayyana cewa ta karɓi ƙudirin daga hannun Gwamna, ta sanar da shi a zaurenta tare da tsara lokacin tattauna shi, amma gabatar da ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2027 ne ya sa aka ba shi fifiko. Hakan na ƙunshe cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa Labaran majalisar, Malam Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar ranar Alhamis, 19 ga Nuwamba, 2026. Majalisar ta ce bin tsarin aikinta ne ya haifar da jinkirin, tare da shawartar Muhyi Magaji da ya nemi ƙarin bayani kan ayyukanta kafin yin irin waɗannan kalamai a bainar jama’a.