Addini
Nagode wa hukumomin Saudiyya da suka bani damar shiga Ka’aba – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya samu wata dama ta musamman ta shiga cikin Ka’abah mai alfarma a birnin Makka, yayin da yake kasar Saudiyya domin gudanar da ibadar Umrah.
Tinubu ya gode wa Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, bisa ba shi da tawagarsa damar shiga cikin Ka’abah domin yin addu’a.
Read Also : Danbatta ya buƙaci gwamnan Kano ya naɗa ƙwararren ɗan jarida a matsayin kwamishinan yaɗa labarai
Shugaban ya bayyana damar shiga Ka’abah a matsayin babban abin alfahari da tarihi, yana mai cewa ya ji dadin wannan dama da aka ba shi. Sheikh Dahlulah Muthawal na Masjid al-Haram ne ya jagorance shi zuwa cikin Ka’abah.
Tinubu ya ce a lokacin da yake cikin Ka’abah, ya gode wa Allah bisa damar da ya ba shi ta jagorantar Najeriya, tare da rokonSa hikima da juriya domin ci gaba da yi wa al’ummar kasar hidima.
Pingback: Na ƙalubalanci Tinubu ya zo mu yi gasar karatun Al-Qur'ani - Dino Melaye - KAKAKI 24