Featured
Idan har Janar Buhari bai iya magance matsalar tsaro ba, me kuke tsammanin Tinubu zai yi? — Yari

Sanata Abdulaziz Yari, Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, ya ce bai kamata a ɗora wa Shugaba Bola Tinubu kaɗai alhakin matsalar rashin tsaron da ƙasar ke fuskanta ba.
Yari ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara jihar Kebbi, inda ya gana da Gwamna Nasir Idris, sarakunan gargajiya da sauran shugabannin APC a Birnin Kebbi. Ya ce tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, wanda Janar ne mai ritaya, ya yi ƙoƙari wajen yaƙi da rashin tsaro amma shi ma bai iya kawar da matsalar gaba ɗaya ba.
Read Also : Buhari ya san Tinubu bai dace da mulkar Najeriya ba shiyasa ya ƙi goyon bayansa – Hakeem Baba-Ahmed
Ya ce gwamnatin Tinubu ma tana yin iya ƙoƙarinta wajen magance matsalar tsaro, yana mai cewa idan Janar Buhari bai samu damar kawar da ita gaba ɗaya ba, ba za a yi tsammanin Tinubu zai magance ta nan take ba. Yari ya kuma ce ya kamata ’yan Najeriya su duba alaƙarsu da Allah tare da ɗaukar nauyin magance matsalar tare da gwamnati.
A ɓangaren tattalin arziki, Yari ya ce matsin rayuwar da ’yan Najeriya ke fuskanta ba matsala ce ta Najeriya kaɗai ba, yana mai cewa hauhawar farashin kayayyaki ta ragu, yayin da farashin taki ya kuma sauka. Gwamna Nasir Idris ya ce jihar Kebbi za ta ci gaba da goyon bayan APC da Shugaba Tinubu gabanin zaɓen 2027.
Pingback: Babu dalilin da zai sa na dawo da tallafin man fetur - Tinubu - KAKAKI 24