Featured
Yaron Da Ya Yi Jawabi Mai Ƙayatarwa a Taron Ƙaddamar da Littafin Garba Shehu Ya Samu Gurbin Karatu Daga Firamare Zuwa Jami’a

Wani yaro da aka sanya masa suna Muhammadu Buhari ya samu cikakken tallafin karatu daga matakin firamare har zuwa jami’a, bayan ya burge mahalarta wajen kaddamar da littafin tsohon mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu.
A wata sanarwa da Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi 13 ga Yuli, ya bayyana cewa shugaban kamfanin Trobell Nigeria, Alhaji Lawal Garba, ne ya bayar da tallafin karatunga yaron, kuma ya amince ga duk wata makaranta da iyayen yaron suka zaɓa.
Yaron, mai suna Muhammadu Buhari, ya ja hankalin kowa a wajen kaddamar da littafin mai taken “According to the President: Lessons from a Presidential Spokesman’s Experience” a ranar 9 ga Yuli a birnin Abuja, inda ya gabatar da jawabi mai taken “Buhari a Cikinmu”.
Yaron, sanye da farar babban riga da jan hula, ya tsaya da kwarin gwiwa gaban mahalarta, inda yayi jawabin sa cikin bege da shauƙi.
A cikin jawabin nasa, yaron ya yabawa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa halayensa na gaskiya, jarumta, da saukin hali, yana kuma kira ga shugabannin Najeriya da su rungumi irin waɗannan halaye wajen hidimar ƙasa.
Jawabinsa ya samu gagarumar maraba da tafi, inda ya zama abin koyi cewa ko da ƙaramar murya na iya tayar da kira zuwa gaskiya da gina ƙasa.
Garba Shehu ya bayyana tallafin karatun a matsayin alamar bege da kyakkyawar makoma ga yaro mai hazaka wanda ya shige zukatan mahalarta da hikimar kalamansa.
A cewarsa: “Lokacin da aka kaddamar da littafina, wani yaro mai suna Muhammadu Buhari ya ja hankalin dukkan mahalarta. “Ta hanyar kamanninsa da tsohon shugaban kasa, da kuma yadda yake magana da nutsuwa, da kuma yadda ya karanta baitin da ke cike da zurfi da bege, ya zama abin kallo a wajen.
“Sakamakon wannan kyakkyawar al’amari, Alhaji Lawal Garba, shugaban kamfanin Trobell Nigeria, ya ba wannan yaro mai hazaka cikakken tallafin karatu.
“Tallafin zai rufe ragowar karatunsa na firamare, sannan za a biya gaba ɗaya kuɗin makarantar sakandare na tsawon shekaru shida, a kowace makaranta da iyayensa suka zaɓa.
“Iyayen yaron sun samu shawarar da su tattara adadin kuɗin da ake bukata su gabatar. In sha Allah, idan ya kammala jarabawar WAEC, za a ci gaba da daukar nauyin karatunsa a jami’a.”
Garba Shehu ya kuma yi kira ga sauran ‘yan Najeriya masu hannu da shuni da su yi koyi da wannan kyakkyawan aiki.
Sanarwar ta ƙare da cewa: “Wannan bai tsaya iya tallafin karatu ba. Wannan shi ne dasa irin bege, gane basira, da saka hannun jari a makomar yaro wanda hazakarsa ta haskaka dakin da ke cike da shugabanni, jakadu, ‘yan jarida da ‘yan ƙasa.
“Muna jinjina sosai ga Alhaji Lawal Garba bisa wannan kyauta, wanda ya tabbatar da cewa idan ka zaburar da mutum, ya kamata ka tallafa masa.