Featured
Tinubu Ya Kammala Jami’a Da Digiri Mai Daraja Ta Farko – Ministan Ilmi

Ministan Ilimi na Najeriya, Tunji Alausa, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kammala karatunsa a Jami’ar Chicago State da ke Amurka da digiri mai daraja ta farko (First Class) a fannin lissafin kuɗi (Accounting).
Ministan ya ce yana da cikakkiyar masaniya kan jami’ar, kasancewar ya shafe kusan shekaru 30 yana zaune a birnin Chicago, inda ya kuma gana da wasu mutanen da suka yi karatu tare da Shugaba Tinubu.
Read Also : Abdul El-Sayed Ya Zama Musulmi Na Farko Da Ya Zama Sanata a Amurka
Alausa ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Talata, inda yake mayar da martani kan tambayoyi game da takardun shaidar karatun shugaban ƙasar.
Ya kuma yi amfani da damar wajen kare sahihancin takardun karatun Tinubu, musamman dangane da ce-ce-ku-cen da aka daɗe ana yi kan tarihin karatunsa a jami’ar ta Chicago.