Featured
Najeriya na asarar maƙuden kuɗaɗe saboda haramta tabar wiwi – Sowore

Dan rajin kare haƙƙin bil’adama kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, Omoyele Sowore, ya yi kira da a halatta noman da sayar da tabar wiwi a Najeriya domin gwamnati ta riƙa samun kuɗaɗen shiga ta hanyar haraji.
Sowore ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata, inda ya ce Najeriya na asarar ɗimbin kuɗaɗe, yayin da wasu ƙasashe ke samun biliyoyin daloli daga sana’ar. Ya ce idan aka halatta ta, Najeriya na iya samun dala miliyan 550 zuwa biliyan 2.2 a duk shekara.
Read Also : Atiku ya yi alkawarin magance matsalar tsaro, farfado da tattalin arziki idan aka zaɓe shi
Ya ƙiyasta cewa kuɗaɗen za su kai naira biliyan 715 zuwa tiriliyan 2.86, bisa la’akari da canjin dala kan naira 1,300. Ya kuma bayar da misalan Kanada da jihohin California da Colorado na Amurka, waɗanda ya ce sun samu biliyoyin daloli daga harajin tabar wiwi a shekarar 2024.
Sowore ya ce halatta sana’ar na iya samar da guraben ayyukan yi a fannonin noma da masana’antar magunguna, tare da bunƙasa binciken kimiyya da fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje. Sai dai ya jaddada cewa kuɗaɗen hasashe ne, kuma tun daga shekarar 2018 yake kira da a duba damar tattalin arzikin sana’ar, duk da cewa noman, sayarwa, mallaka da amfani da tabar wiwi haramun ne a Najeriya.
Pingback: Wike ga ’yan APC: Kada ku bari ADC da NDC su samu kashi 25 cikin 100 na ƙuri’u a Abuja - KAKAKI 24