Featured
Mun samu masu son saka hannu jari a matatar mu daga kasashe 120 na duniya – Dangote

Matatar Mai ta Dangote ta ce ta samu masu neman zuba jari daga ƙasashe 120 na duniya, ciki har da dukkan ƙasashe 54 na Afirka, bayan rufe shirin sayar da hannayen jarinta a ranar Talata.
Kamfanin ya bayyana hakan a matsayin babban ci gaba ga kasuwannin hannun jari na Afirka, inda ya ce tayin ya samu masu zuba jari daga dukkan nahiyoyi shida na duniya.
Read Also : Zan iya sadaukar da rayuwata wajen ganin Tinubu ya yi nasara a 2027 – Uba Sani
Shugaban Dangote Industries Limited, Alhaji Aliko Dangote, ya ce yadda aka amsa tayin ya nuna cewa ’yan Afirka na da niyyar zuba jari a masana’antun da aka gina a nahiyar domin cin gajiyar ci gaban masana’antu.
Shi ma Babban Jami’in Gudanarwa na kamfanin, David Bird, ya ce martanin masu zuba jarin na nuna ƙwarin gwiwarsu ga girman matatar, ƙwarewar gudanar da ayyukanta da kuma burinta na gaba.
Pingback: Gwamnatin Tinubu ta amince da ba wa ma’aikata tallafin 70,000 duk wata na tsawon watanni shida - KAKAKI 24