Connect with us

Featured

Bauchi: Dalibin JSS3 Ya Kirkiri Fasahohin Da Za Su Taimaka Wa Al’umma

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Wani dalibin aji uku na ƙaramar makarantar sakandare (JSS3) a Ummul-Qura Science Academy da ke Azare, ƙaramar hukumar Katagum a jihar Bauchi, Hayatuddeen Sadik Bello, ya ƙware wajen ƙirƙirar wasu fasahohin da ke da nufin taimaka wa al’umma wajen rage wasu daga cikin wahalhalun rayuwar yau da kullum.

Dalibin ya bayyana hakan ne a yayin taron bai wa ɗalibai masu hazaka kyaututtuka domin ƙara musu ƙwarin gwiwa kan karatunsu, wanda makarantar ta gudanar a harabar ta da ke garin Azare. A yayin taron, Hayatuddeen ya baje kolin wasu daga cikin abubuwan da ya ƙirƙira da hannunsa, tare da nuna yadda suke aiki a aikace.

Daga cikin abubuwan da ya ƙirƙira akwai murhun girki mai amfani da ruwa da fetur, samfurin jirgin Jet, samfurin helikwafta, mota mai amfani da iskar gas, jirgin ruwa, injin niƙa da sauran kayayyakin fasaha. Ya kuma bayyana cewa babban burinsa a nan gaba shi ne ƙirƙirar sabbin hanyoyin samar da makamashi, ciki har da makamashin da za a iya samarwa daga kashin shanu, tare da ƙirƙirar motar kashe gobara domin taimakawa wajen rage wasu daga cikin ƙalubalen da al’umma ke fuskanta, musamman sakamakon tsadar man fetur da iskar gas.

«“Ni burina nan gaba shi ne samar da sabbin hanyoyin kimiyya da za su sauƙaƙawa al’umma ayyukan yau da kullum, tare da taimakawa wajen magance wasu matsalolin da suke fuskanta,” in ji Hayatuddeen.»

Read Also : PDP ta sauya sunan ɗan takarar gwamnan Kano da Muhammad Sani Abacha

Da wakilinmu ya tuntubi mahaifin dalibin, Abubakar Sadik Bello, domin jin yadda ya ji lokacin da aka sanar da cewa ɗansa ya zama zakara wajen ƙirƙire-ƙirƙiren fasaha, ya bayyana farin cikinsa da cewa ba zai iya misalta irin farin cikin da ya ji ba.

«“Wallahi ban san lokacin da ƙwalla suka zubo daga idona ba, saboda tsananin farin cikin da na ji. A ganina, wannan nasara ba ta ɗana ba ce kawai, ta kowa ce,” in ji shi.»

Malam Abubakar ya gode wa Allah SWT da Ya bai wa ɗansa wannan baiwa ta fasaha, wadda ta kai shi ga samun ilimin ƙirƙire-ƙirƙire tun yana aji uku na ƙaramar sakandare. Ya kuma yaba wa malaman Ummul-Qura Science Academy bisa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen horar da ɗalibai da haɓaka basirarsu.

Tun da farko, hukumar makarantar ta bayyana cewa tana shirya irin wannan taro ne domin karrama ɗalibai masu hazaka da ba su kyaututtuka, a matsayin hanyar ƙara musu ƙwarin gwiwa da kuma ƙarfafa sauran ɗalibai su mayar da hankali wajen karatu da bunƙasa basirarsu. Taron na bana ya haɗa da Speech and Prize-Giving & Qur’anic Memorization, inda aka karrama ɗaliban da suka nuna ƙwazo a fannoni daban-daban na karatu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet