Featured
Mutuwar Matasa a Neja: Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shugaban NSCDC na Jihar

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin dakatar da Shugaban Hukumar Tsaron Fararen Hula da Kare Haƙƙin Jama’a ta Najeriya (NSCDC) a jihar Neja, Suberu Aniviye, sakamakon mutuwar wasu matasa da ake zargin masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba ne.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayar da umarnin a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya buƙaci gudanar da cikakken bincike kan lamarin da rahotanni suka ce ya faru a yankin Wushishi/Lukoto da ke Minna.
Sanarwar ta ce an kama waɗanda ake zargin masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba ne yayin samamen da aka gudanar a wasu yankunan jihar a ranar Talata da Laraba. Ministan ya kuma buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da bin doka da oda.
Tun da farko, gwamnatin jihar Neja ta ce an kama kwamandan hukumar. Rahotanni sun ce jami’an hukumar sun kama matasan bisa zargin haƙar zinare ba bisa ƙa’ida ba, yayin da da farko jami’ai suka yi hasashen cewa wata cuta ce ta haddasa mutuwarsu, sai dai rahotanni sun nuna cewa cunkoso da rashin isasshen iska a wurin da ake tsare da su ne ya yi sanadin mutuwar.
Pingback: Gwamnatin Neja ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Minna - KAKAKI 24