Featured
Abdul El-Sayed Ya Zama Musulmi Na Farko Da Ya Zama Sanata a Amurka

Ɗan jam’iyyar Democrat, Abdul El-Sayed, ya samu nasarar lashe zaɓen kujerar Sanatan Amurka mai wakiltar jihar Michigan, kamar yadda hasashen kafafen yaɗa labarai ya nuna.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa nasarar tasa ta sanya shi zama musulmi na farko da aka taɓa zaɓa zuwa Majalisar Dattawan Amurka.
Read Also : Dangote Cement Obajana Scales Up Scholarship Funding For Oworo Students
Wannan nasara ta zo ne a daidai lokacin da jam’iyyar Democrat ke ƙoƙarin ƙara yawan kujerunta a Majalisar Dattawan ƙasar, domin ƙarfafa matsayinta na siyasa.
Sai dai rahoton ya bayyana cewa nasarar El-Sayed na da muhimmanci a tarihin wakilcin musulmi a siyasar Amurka, musamman kasancewarsa na farko da ya samu wannan matsayi a Majalisar Dattawa.
Pingback: Tinubu Ya Kammala Jami’a Da Digiri Mai Daraja Ta Farko - Ministan Ilmi - KAKAKI 24