Featured
Amurka ta ci amanarmu – Shugaban Ukraine

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce yana jin Amurka ta ci amanar ƙasarsa, bayan da Shugaba Donald Trump ya janye takunkumin da aka kakaba wa man dizal na Rasha.
Zelensky ya kuma ce Trump ya sanar da tsagaita hare-hare kan cibiyoyin makamashi, amma Rasha ta yi watsi da yarjejeniyar.
Read Also : Arc. Aminu Dabo ya fice daga jam’iyyar APC
AYayin wata hira da ɗan jaridar Birtaniya Piers Morgan ta talabijin, Zelensky ya ce alamun da ake gani na nuna cewa Kyiv ta rasa goyon bayan Amurka na dogon lokaci a yaƙin da take yi da Rasha.
Ya kuma bayyana damuwarsa kan yiwuwar Amurka ta ƙara taƙaita bayanan sirrin da take bai wa Ukraine, sai dai Donald Trump ya musanta hakan.
Pingback: Ba mu hana ɗalibai mata masu niƙabi shiga makaranta ba - Kwale jin Shari'a ta Aminu Kano - KAKAKI 24