Featured
Ba’a Samu Asarar Rai A Hatsarin Jirgin Air Peace Ba — FAAN

Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) ta tabbatar cewa ba a samu asarar rai ba a hatsarin da ya faru da jirgin Air Peace mai lamba P47190 da ya taso daga Legas zuwa Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa da ke Fatakwal.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktar Hulɗa da Jama’a da Kare Haƙƙin Fasinjoji na FAAN, Obiageli Orah, ta fitar a ranar Lahadi a Legas.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi 13 ga Yuli, 2025.
A cewar Orah, jirgin da ke ɗauke da lambar rajista 5N-BQQ ya tashi daga Legas sannan ya sauka a Filin Jirgin Sama na Fatakwal da misalin ƙarfe 7:45 na safe.
Ta bayyana cewa jirgin ya ketare titin saukar jirgi (runway 03) lokacin da yake sauka.
Orah ta ce: “Muna murna da sanar da cewa ba a samu asarar rai ba.”
A halin yanzu, ta bukaci fasinjoji su yi shirin jinkiri ga duk wasu tafiye-tafiyen jirage da za su tashi zuwa Fatakwal.
Ta kuma ƙara da cewa akwai karin bayani da za a bayar idan da bukata.
Orah ta sake jaddada cewa FAAN na ɗaukar tsaron fasinjoji da lafiyar su da matukar muhimmanci.