Featured
Ba don Tinubu ba, da Buhari bai zama shugaban Najeriya ba – Shettima

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya ce da ba don taimakon Shugaba Bola Tinubu ba, marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba zai samu nasarar shugabancin Najeriya ba.
Shettima ya bayyana hakan ne a jawabinsa yayin taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen Tinubu na wa’adin mulki na biyu a jihar Kaduna.
Read Also : Zaɓen 2027 : Ni ba ɗan siyasa bane, don haka babu ɗan takarar da zan yi wa yakin neman zaɓe – Daurawa
Ya ce Tinubu ya taimaka wa ‘yan Arewa a lokuta daban-daban wajen neman shugabancin ƙasar, ciki har da Atiku Abubakar da ya taimaka masa a AD, da Nuhu Ribadu a AC, da kuma Buhari a zaɓen 2015 da 2019.
Shettima ya ce kasancewar Tinubu ya bayar da gudunmawa ga ‘yan takarar Arewa a baya, yanzu lokaci ya yi da za a mayar masa da wannan alheri.
Pingback: Ƴan adawa ne suka jefa Najeriya cikin yunwa da talauci - Tinubu - KAKAKI 24