Connect with us

Featured

ASUU ta umarci malaman jami’o’i su shirya tsunduma yajin aiki

Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU) ta umarci malaman jami’o’i 20 da su fara shirye-shiryen shiga yajin aikin gama-gari, bisa zargin gazawar gwamnatin tarayya da wasu gwamnatocin jihohi wajen cika yarjejeniyar da suka kulla da ƙungiyar a shekarar 2025.

ASUU ta bai wa gwamnatocin da abin ya shafa wa’adin makonni biyu domin magance matsalolin da suka rage. Shugaban ASUU na shiyyar Kano, Dakta Abdulrazaq Ibrahim Fagge, ya ce an ɗauki matakin ne bayan taron uwar ƙungiyar a Abuja, sakamakon ƙorafe-ƙorafen da aka samu daga wasu jami’o’i.

Read Also : Ba Tinubu nake tallatawa ba, Musulunci nake tallatawa – Sheikh Jingir

Fagge ya ce duk da yarjejeniyar da aka cimma a Disambar 2025 kan sabbin alawus-alawus da sauye-sauyen tsarin jami’o’i, wasu gwamnatocin jihohi ba su aiwatar da abin da suka amince da shi ba. Ya ce gwamnatin tarayya kuwa ta fara cika nata alƙawuran tun daga Janairun wannan shekarar.

ASUU ta zargi wasu gwamnatocin jihohi da fifita wasu ayyuka kan ilimi, tana mai cewa ba ta shirya sake zama da gwamnati a yanzu ba bayan shafe watanni takwas ana tattaunawa. Ta gargadi cewa rassan da abin ya shafa za su shiga yajin aiki idan wa’adin makonni biyun ya cika ba tare da an warware matsalolin ba.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet