Featured
Fursunoni 58 Sun Rubuta Jarabawar NECO a Kano — NCoS
Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) reshen Jihar Kano ta bayyana cewa fursunoni 58 daga cibiyoyin gyaran hali a jihar na halartar jarabawar kammala sakandire ta NECO na shekarar 2025.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Kofar-Nasarawa, ya fitar a ranar Lahadi 06 ga Yuli 2025, a Kano.
A cewarsa, wannan ci gaban ya samu ne sakamakon biyan kudin rajista da gwamnatin jihar Kano ta yi karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
“Wannan karamci na nuna irin jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da jin daɗi, gyara hali, da kuma dawo da fursunoni cikin al’umma,” in ji Kofar-Nasarawa.
Hukumar ta nuna godiya ta musamman ga Gwamnan bisa wannan goyon baya mara yankewa, tana mai cewa hakan zai kara wa fursunonin kwarin gwiwa.
“Hukumar NCoS reshen Jihar Kano na ci gaba da jajircewa wajen samar da yanayi mai kyau domin gyara hali da koyar da fursunoni.
“Muna alfahari da samun irin wannan goyon baya daga Gwamnatin Jihar Kano a wannan aiki mai muhimmanci,” in ji sanarwar.
NAN
