Connect with us

Featured

‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 4 Da Ake Zargi Da Kai Hari Fadar Sarkin Kano

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane huɗu da ake zargi da hannu a harin da aka kai fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu, a cikin birnin Kano, a ranar Lahadi 06 ga Yuli, 2025.

Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da kama waɗanda ake zargin, cikin saƙon da ya aike wa jaridar The PUNCH ta hanyar WhatsApp a ranar Talata 08 ga Yuli, 2025.

Ya ce, “Eh, runduna ta kama mutane huɗu kuma suna tsare a hannun ‘yan sanda yayin da bincike ke gudana.”

A cewarsa, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Bakori, ya kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin tashin hankali da ya faru tsakanin magoya bayan Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da na Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II.

Jaridar The PUNCH ta ruwaito a baya cewa, an kusa samun rikici mai tsanani a ranar Lahadi lokacin da wasu magoya bayan Aminu Ado Bayero da na Muhammadu Sanusi II suka yi arangama a Kofar Kudu da ke cikin birnin Kano.

Lamarin ya faru ne yayin da wasu matasa da ake zargin magoya bayan Sanusi ne suka toshe hanya domin hana Aminu Ado Bayero wucewa ta hanyar Kofar Kudu yayin da yake komawa fadar Nasarawa bayan ya kai ziyartar ta’aziyya ga dangin marigayi attajirin Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

Biyo bayan faruwar lamarin, rahotanni sun bayyana cewa wasu masu gadi na fadar sun jikkata, an kuma lalata wasu motocin ‘yan sanda da ke gadin fadar, tare da lalata babbar ƙofar shiga fadar.

 

 

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet