Connect with us

Addini

NAHCON Ta Fara Shirye Shiryen Aikin Hajjin 2026

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta fara shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2026, bayan kammala aikin Hajjin 2025 cikin nasara.

Shugaban NAHCON, Alhaji Abdullahi Pakistan, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano, jim kadan bayan dawowarsa daga Saudiyya a ranar Alhamis 10 ga Yuli, 2025.

“Mun samu umarni daga hukumomin Saudiyya cewa ba za su jira kowace kasa ba wadda bata kammala shirye-shiryenta da wuri ba. Sun bukaci a kammala dukkanin shirye-shirye akan lokaci,” inji shi.

“Muna neman amincewa domin mu sanar da kudin Hajji na shekarar 2026 nan bada jimawa ba. Don haka muna rokon dukkan ’yan Najeriya da ke da niyyar zuwa Hajji da su yi rijista da wuri.”

Pakistan ya bayyana godiya ga Allah Madaukakin Sarki saboda gudanar da aikin Hajji cikin nasara da kuma dawowar alhazai lafiya, tare da mika godiya ga Gwamnatin Tarayya, musamman Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaba Kashim Shettima saboda goyon bayan da suka bayar.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet