Connect with us

Featured

Tinubu Zai Ziyarci Kano A Gobe Juma’ah Domin Ta’aziyyar Ɗantata

Jihar Kano ta kammala shirye-shiryen tarbar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu GCFR a ranar Jumma’a, 18 ga Yuli, 2025, domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Kano, da kuma iyalan marigayi dattijo, hamshaƙin ɗan kasuwa kuma mai bayar da gudummawa ga al’umma, marigayi Alhaji Aminu Dantata.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Alhamis 17 ga Yuli, 2015.

Ziyarar na zuwa ne biyo bayan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa wanda ya bar tarihi mai girma na hidima, kyauta, da zuba jari wanda ya shafi rayuwar dubban ‘yan Najeriya tsawon shekaru da dama.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana wannan ziyara a matsayin alamar haɗin kai na da girmamawa ga al’ummar Kano da kuma tarihin marigayi Alhaji Aminu Alasan Dantata.

Ya yi kira ga mazauna Kano da su tarbi Shugaban Ƙasa cikin mutunci da al’adun girmamawa da martaba da jihar ke alfahari da su.

“Wannan lokaci ne na yin tunani mai zurfi da kuma nuna girmamawa,” in ji Gwamna Yusuf.

“Ina kira ga kowane ɗan jihar Kano da ya tarbi Shugaban Ƙasa cikin farin ciki da tsari, yayin da ya zo mana domin jajanta rasuwar ɗaya daga cikin manyan dattawanmu.”

An tanadi tsaro da sauran shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da kyakkyawan yanayin don ganin an gudanar da wannan ziyara cikin lumana.

 

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet