Connect with us

Featured

ASUU Za Ta Kai Gwamnatin Tarayya Ƙara Bayan Sauya Sunan UNIMAID Zuwa Muhammadu Buhari University

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), reshen Jami’ar Maiduguri (UNIMAID), ta bayyana ƙin amincewarta da kuma ƙin lamuntar sauya sunan jami’ar zuwa Muhammadu Buhari University, da gwamnatin tarayya ta yi, tare da shaida cewa za ta dauki matakin shari’a kan lamarin.

A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Abubakar Mshelia, da mataimakin sakataren ƙungiyar, Peter Teri, suka sanyawa hannu a ranar Juma’a 25 ga Yuli, ASUU ta ce matsayar ta biyo bayan wani taron gaggawa da ta gudanar a ranar 24 ga Yuli, 2025.

Ƙungiyar ta bayyana cewa taron ya samu halartar mambobin ASUU, wakilan dalibai daga ƙungiyar SUG (Student Union Government), da wasu muhimman masu ruwa da tsaki a harkar jami’ar.

Sanarwar ta ce: “Bayan tattaunawa mai zurfi, taron ya yanke shawarar kin amincewa da kuma yin Allah-wadai da yunkurin sauya sunan University of Maiduguri zuwa Muhammadu Buhari University, Maiduguri.”

“Taron ya bayyana wannan yunkuri a matsayin sabawa dokokin ikon gudanar da jami’o’i (university autonomy), da ƙetare al’adun ilimi da suka dade ana kiyayewa, da kuma cin zarafin tarihin da martabar jami’ar ke da shi na sama da shekaru 50.”

ASUU ta bayyana matakin gwamnatin tarayya a matsayin: Shisshigi, Yanke hukunci ba tare da neman shawara daga cikin gida ba, da kuma rashin girmamawa ga tsari da masu ruwa da tsaki.

Ƙungiyar ta bayyana cewa an ba wa shugabancin ASUU-UNIMAID izini su binciko duk wata hanya ta doka domin dakile wannan sauyi da kuma kare asalin martabar jami’ar.

Haka kuma, kungiyar ta bukaci: Dukkan sassan ASUU na ƙasa, Cibiyoyi na ƙungiyoyin fararen hula (CSOs), Dalibai da sauran masu ruwa da tsaki. Su tashi tsaye wajen kin amincewa da duk wani yunkuri na majalisar dokoki da zai goyi bayan sauya sunan.

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet