Connect with us

Featured

Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Yi Ajalin Ƴan mata 9 A Jigawa

Mutane tara 9 sun rasa rayukansu daga cikin mutum 17 da ibtila’i ya rutsa da su, a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa, yayin da wasu takwas 8 suka tsira.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ce ta tabbatar da hakan a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a ranar Alhamis 31 ga Yuli, 2025.

A cewar ofishin NEMA na Kano, hatsarin ya faru ne ana tsaka da tafiya daga kauyen Digawa da ke ƙaramar hukumar Jahun zuwa kauyen Zangon Maje a karamar hukumar Taura.

Sanarwar mai taken: “NEMA Kano ta gudanar da bincike kan hatsarin jirgin ruwa a kauyen Zangon Maje, ƙaramar hukumar Taura, jihar Jigawa – 30 ga Yuli, 2025”.

“Hukumar NEMA, shiyyar Kano, ta kai ziyara domin duba hatsarin jirgin ruwa da ya faru a kauyen Zangon Maje da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa.

“Bincike ya nuna cewa hatsarin ya faru ne a ranar Lahadi, 27 ga Yuli, 2025, da misalin ƙarfe 7:00 na dare. Jirgin, wanda ke ɗauke da fasinjoji 17 – mafi yawancinsu ‘yan mata – ya kife ana tsaka da tafiya daga kauyen Digawa a Jahun zuwa Zangon Maje a Taura.

“Lokacin da tawagar NEMA ta isa wurin, an tabbatar da cewa mutane takwas (8) an ceto su da ransu, yayin da mutum tara (9) aka tabbatar da mutuwarsu.”

Hukumar NEMA ta ce tana aiki tare da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (JSEMA), da Hukumar Kula da Ruwa ta Ƙasa (NIWA), da kuma jami’an ƙaramar hukumar wajen wayar da kan jama’a dangane da muhimmancin bin ƙa’idojin tsaro yayin amfani da hanyoyin ruwa.

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet