Connect with us

Featured

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kaddamar da Rabon Bishiyoyi Miliyan 5.5 Don Yaki da Kwararowar Hamada

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da rabon shukar itatuwa miliyan 5.5 a fadin jihar domin dakile yaduwar hamada da kuma inganta dorewar muhalli.

An gudanar da bikin kaddamarwar ne a ranar Lahadi 03 ga Agusta, a filin shuka itatuwa na tarihi na Yanbawa Shelter Belt da ke karamar hukumar Makoda.

Gwamna Yusuf ya bayyana cewa dukkan kananan hukumomi 44 na jihar za su samu kason nasu na itatuwan da za a raba zuwa makarantu, al’ummomi da sauran hukumomin da suka dace.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi.

Gwamna ya ce: “Mun taru a nan yau a wurin shuka itatuwa na tarihi na Yanbawa da ke Makoda, wanda tsohon Gwamnan Soja, Marigayi Audu Bako, ya kafa a shekarar 1972.”

Ya bayyana wurin a matsayin daya daga cikin tsofaffi kuma mafi ƙarfi wajen dakile yaduwar hamada, yana mai jaddada irin rawar da ya dade yana takawa wajen kare muhalli.

Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda aka yi watsi da wuraren shuka itatuwa da na noman shuka a shekarun baya, amma ya yaba da kokarin gwamnatinsa wajen farfado da su cikin gaggawa.

“Kafin shekarar 2023, babu wata cibiyar shuka itatuwa da ke aiki yadda ya kamata a jihar. Amma mun gyara manyan cibiyoyi guda biyu — daya a Mai Nikka (Gwarzo), daya kuma a Kafinciri (Garko) — domin amfanin jama’a.”

Don tabbatar da nasarar shirin, Gwamna Yusuf ya umurci dukkan shugabannin kananan hukumomi da su kafa Kwamitocin Shuka Itatuwa a karkashin sashen harkokin noma na kowacce gwamnati.

Ya kuma bayar da umarnin shuka itatuwa a makarantu, cibiyoyin addini da kan tituna domin samar da muhalli mai tsafta.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet