Featured
Babu Wani Batun Ƙawance Domin Tinubu Ya Ci Amanar Kwankwaso a Kano – Buba Galadima
Babban jigo a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Buba Galadima, ya yi watsi da duk wata yiwuwar haɗin gwiwa tsakanin shugaban jam’iyyarsu, Rabiu Musa Kwankwaso, da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta Shugaba Bola Tinubu.
Da ya ke magana kan rikicin da ake fama da shi a Kano kan masarautu, Galadima ya ce :
“Ta yaya Kwankwaso zai zama abokin APC bayan irin abin da suke yi mana a Kano? Sun nada sarakuna biyu a gari guda. Akwai Sarkin Gwamnatin Tarayya da Sarkin Jiha. Wa ke da hurumin naɗa sarakai kuma ya rika biyansu albashi?”
Ya kuma zargi gwamnati da amfani da jami’an tsaro wajen goyon bayan wani sarki, alhali a wasu yankuna na Kano ana kashe mutane ana kuma kwace wayoyinsu, amma ‘yan sanda sun mayar da hankali kawai wajen tsaron sarki.
“Suna da sarakunansu. Suna da akalla motoci ‘yan sanda pickup 40 cike da Mobile Police suna tsaron (Ado Bayero). A wasu unguwanni a Kano ana kashe mutane ana kwace musu wayoyi, amma ‘yan sanda suna zaune su na gadin Aminu Ado. Shin ba sa jin kunya?” a cewar Galadima.
Buba ya kuma yi watsi da jita-jitar cewa Kwankwaso na tattaunawa da Tinubu, yana mai bayyana tsohon gwamnan Kano a matsayin ƙarfen ƙafa a siyasa.
“ Ta yanya za a gaya min cewa ya gana da Kwankwaso ya kuma shawo kansa ko ya tilasta masa shiga APC. Da a ce an yi haka, da ni na sani. Shi ne mutumin da ya fi kowa karfi a siyasar wannan ƙasa yau.”
Ya kuma yi zargin cewa gwamnati ta tarayya tana amfani da ‘yan sanda da kotuna wajen rikita Kano domin kawai ta raunana tafiyar Kwankwaso kafin 2027.
