Connect with us

Featured

Rahoton Amurka: Albashin N70,000 Ba Zai Fitar da ‘Yan Najeriya Daga Talauci Ba

Gwamnatin Amurka ta bayyana damuwa kan sabon mafi ƙarancin albashi na Najeriya, inda ta ce N70,000 da aka amince da shi bai isa ya fitar da al’umma daga talauci ba, saboda tabarbarewar tattalin arziƙi da hauhawar farashi.

A cikin Rahoton Ƙasashe kan Hakkokin Dan Adam na 2024 da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar a ranar 12 ga Agusta 2025, an bayyana cewa sabon albashin da yanzu bai kai $48 a wata ba (saboda faduwar naira da ke sama da N1,500/$1), ya ragu ƙwarai wajen amfani.

Rahoton ya nuna cewa duk da cewa dokar albashi ta 2024 ta ninka tsohon albashi, sai dai ba’a bawa dokar muhimmanci yadda ya kamata ba. Jihohi da dama sun ƙi bin dokar saboda ƙarancin kuɗi, kuma gwamnatin tarayya ba ta tsaurara mataki akai ba.

Bugu da ƙari, dokar ta shafi kamfanoni da ke da ma’aikata 25 ko fiye. Ma’aikatan wucin gadi, na noma, da masu kwangilar kashi-kashi basa daga cikin tanadin.

Haka kuma, tsakanin kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na ma’aikata a Najeriya na aiki ne a sashen informal, inda dokokin albashi, lokaci, da tsaron muhalli ba sa aiki yadda ya kamata. Yawan masu duba aiki a gwamnati kuwa bai isa ba, abin da ya bar ma’aikata da dama cikin hadarin cin zarafi.

Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke cikin sauye-sauyen tattalin arziƙi – cire tallafin man fetur da daidaita farashin dalar Amurka – matakan da suka haifar da hauhawar farashi da tsadar rayuwa ga talakawa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet