Featured
Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Yi Ajalin Mutane 60 A Neja
Wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a gabar kogin Malale, karamar hukumar Borgu a jihar Neja, ya yi ajalin akalla mutane 60. Jirgin mai ɗauke da sama da mutum 90 ya tashi daga Tugan Sule a Shagunu, yana kan hanyarsa ta zuwa Dugga domin halartar gaisuwar ta’aziyya.
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safe ranar Talata, 2 ga Satumba, sakamakon yawan fasinjoji da kuma karo da wani itace a cikin ruwa. Hukumar NSEMA ta tabbatar da gano gawarwaki 29 tun farko tare da ceto mutum 50, amma daga baya alkaluman mutanen da suka mutu suka karu.
Shugaban karamar hukumar Borgu, Abdullahi Baba Ara, ya bayyana cewa adadin mamatan ya haura zuwa 60, yayin da wasu mutum 10 ke cikin mawuyacin hali, kuma har yanzu ana ci gaba da neman waɗanda ba a gani ba.
A cewar Sarkin Shagumi, Sa’adu Inuwa Muhammad, jirgin ya ɗauki fiye da mutum 100, inda aka gano gawarwaki 31 daga cikin ruwa, sannan aka binne hudu bisa tsarin Musulunci. Ya ce mafi yawan waɗanda suka rasa rayuka mata ne da yara.
