Featured
Obi Zai Bayyana Matsayarsa Akan ADC Bayan Zaben Gwamnan Anambra
Kungiyar Obidient ta bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, zai yanke hukunci kan shiga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) bayan kammala zaɓen gwamnan Anambra wanda za a yi ranar 8 ga Nuwamba. Shugaban kungiyar, Dakta Yunusa Tanko, ne ya bayyana hakan lokacin da yake hira da jaridar The Punch a ranar Lahadi.
Tanko ya yi wannan bayani ne bayan kiran da mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, wanda ya buƙaci shugabannin gamayyar adawa – ciki har da Atiku Abubakar da Obi – su bar jam’iyyunsu na yanzu su shiga ADC gaba ɗaya. Ya ce ADC ta bai wa Obi damar ɗaukar lokaci ya yi tunani kan shawarar, saboda haka ba za su tilasta masa barin Labour Party yanzu ba.
Ya ƙara da cewa Obi ba zai bayyana matsayinsa kan shiga ADC ba sai bayan kammala zaɓen Anambra, inda kungiyar Obidient ta ce ta fi mayar da hankali kan tallafawa ‘yan takara a wannan zaɓe. A cewarsa, hakan ya fi zama dabara kuma ADC ba ta bayar da wani wa’adi ba. Obi a halin yanzu ya fita kasar waje domin wani aiki, don haka ba zai yanke shawara ba har sai ya gama shawarwari.
A cikin wata sanarwa da Tanko ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa Obi ba mutum ba ne mai hanzari ko son mulki ta kowace hanya, manufarsa ita ce ganin Najeriya ta samu ci gaba a tattalin arziki, ilimi, kiwon lafiya da tsaro. Kungiyar ta kuma nuna damuwa kan yadda ADC ke sauya yarjejeniyar rabon mukamai da tsarin yankuna, tana mai cewa Obi zai ci gaba da tuntubar mabiya da abokan hulɗa kafin ya dauki kowane mataki na siyasa.
